Monday 23 October 2017

National Measles Campaign: Zamfara targets 1.2m children

The Zamfara State Government on Monday said that it was targeting 1.2 million children across the state for the 2017 measles campaign.

The state Commissioner of Health, Alhaji Sulaiman Gummi, disclosed this at a press conference in Gusau.

Gummi said that children aged nine to 59 months would be given the vaccine to prevent them from being affected by measles and other five child killer diseases.

He said that the state government had released N17 million for the exercise through the local government health basket funds under the ministry of local government and chieftaincy affairs.

According to him, the state government and UNICEF have mobilised 1,058 teams to carry out the exercise across the state.

He said Gov. Abdul’aziz Yari had already directed all traditional rulers, civil servants and political office holders to support the exercise in their areas.

He urged members of the public to allow their children to be vaccinated so that the children would grow up in good health.

He commended the support and assistance given to the state health sector by the international donor organizations like UNICEF and WHO.

(NAN)

Also Read ZAMFARA NGOS VOWS TO SCALE UP ADVOCACY ON NUTRITION

Dalilinmu Na Son Canza Fa-salin Makarantun Firamare A Zamfara –Jangebe 

HONARABUL MURTALA ADAMU JANGEBE shi ne Shugaban Hukumar Bayar Da Ilimi Bai Ɗaya ta Jihar Zamfara. Bugu da ƙari shi ne Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Hukumar SUBEB na Nijeriya bakiɗaya, muƙamin da ya samu kansa a bisa ga tarihin da ya kafa na zama mafi daɗewa a kujerar shugabancin Hukumar SUBEB wadda Gwamna Abdu’aziz Yari Abubakar ya naɗa saman muƙamin a Satumba 2011. A wannan tattaunawa da wakilinmu SHARAFADDEEN SIDI UMAR, Jangebe ya yi bayani game da shirin kyautatawa al’umma da ƙoƙarin Hukumarsa na canza fasalin ilimi bai ɗaya domin samu ci-gaba mai amfani da ɗorewa a Jihar Zamfara.

Ko mene ne Gwamnatin Jiha ke yi domin ganin ta ƙarfafa yawaitar sanya yara a makaranta?

Idan za ku iya tunawa a 2011 lokacin da wannan Gwamnatin ta shiga ofis, mun gudanar da aikin musamman na bitar sha’anin ilimin firamare a Zamfara, mun gudanar da bita kan dukkanin sha’anin gudannarwar makarantun firamare a faɗin jiha ciki har da yanayin da malamai suke ciki, ɗakunan karatu, yanayin koyarwa da na kayan karatu, yanayin gine-gine, tsaftar makarantu da sha’anin samar da ruwan sha da sauransu. Mun gudanar da wannan aikin ne domin mu gano abin da ya kamata ya zama ingantacce a sha’anin bayar da ilimi a makarantun firamare a wannan jiha.

Mun fara a 2011 muka kammala a 2012. Bayan kammala aikin mun gano muna da yara 283, 000 kawai a firamare mai makon yara dubu 500 zuwa dubu 600 da ya kamata a ce akwai a firamare. Wannan ya nuna mana halin da sanya yara a makaranta yake ciki.

A lokacin da muka gano wannan matsalar, Gwamnatin Jiha ta bayar da ƙaimi wajen sanya yara makaranta a Satumba 2012 a inda aka umurci Sarakunan Gargajiya da manyan jami’an Gwamnati da shugabannin siyasa da su koma wajen al’ummar su domin su himmatu sosai wajen kamfen ɗin sanya yara makaranta domin a dawo da yaran da suka ƙauracewa makaranta su sake komawa makaranta wanda hakan ya sanya adadin lambar yara ta ƙaru daga 283, 000 zuwa 447, 000 a cikin wata ɗaya kawai, a bisa ga wannan ne adadin yawan yara ‘yan makaranta ke ƙaruwa kuma har zuwa yau yana ƙaruwa.

Haka kuma a kowace shekara muna gudanar da abin da muka kira Ƙidayar Shekara da manufar gano ainihin adadin yaran da ke shiga makaranta. Wata hanya kuma ita ce ta ƙawance wadda muka yi a cikin dai shekarar ta 2011. Ba mu da abokan ƙawancen ci gaba ko guda ɗaya a cikin jiha, amma bisa ga ƙoƙarin mu mun samu nasarar kawo UNICEF, DFID da MC Arthur Foundation. Muna da shirin da muke gabatarwa mai suna RANA wanda ke ƙoƙarin ilmantar da al’umma a cikin Harshen Hausa. A yau muna da abokan hulɗa kusan guda biyar a wannan jihar. Bankin Duniya ma zai zo domin duba matsalar yaran da suka ƙauracewa makaranta.

Zuwa watan gobe wato Satumba za mu himmatu ga shirin bayar da kuɗaɗe ga iyaye ‘yan asalin jiha waɗanda suke kasa ɗaukar nauyin sanya yaransu makaranta. Mun kira shirin da sunan shirin tallafawa. Iyayen da suka amfana za su yi amfani da kuɗaɗen wajen siyawa ‘ya’yan su kayan makaranta da litaffan karatu. Muna da tabbacin wannan shirin zai taimaka wajen ƙara yawan yaran da ke shiga makaranta. Kusan naira milyan 200 ne za a kashe a wannan shirin tare da haɗin guiwa da UNICEF.

Mene ne Hukumar ka ke yi domin ganin ta inganta jin daɗi da walwalar Malamai?

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayar da fifiko ga kyautata jin daɗi da walwalar Malaman Makarantun Firamare. Babu tababa a kan wannan. A wannan hukumar muna kula da walwalar su ta fuskoki biyu. Na farko jihar Zamfara tana ɗaya daga cikin jihohi a faɗin ƙasar nan da ba su taɓa riƙe albashin malamai ba ko da na wata ɗaya ne. Akwai jihohi da dama da ake kasa biyan albashin malamai a tsayin watanni shida zuwa sama.

Amma a Zamfara muna bayar da albashi kan kari da sauran haƙƙoƙin malamai. Baya ga wannan wata hanya ta kyautata masu shi ne inganta aikin malanta. Mun fahimci cewa kyautata jin daɗin malamai ya wuce ɗaukar albashi zuwa gida kawai.

Gwamnatin Jiha tana yin abubuwa da dama ta fuskar horas da malamai, horo mafi inganci a Nijeriya da Ƙasar Waje, muna tabbatar da cewar an horas da su a cibiyoyi masu inganci. A yanzu haka mun ƙulla hulɗa da shirin bunƙasa rayuwar yara na ‘Child Deɓelopment Project’ na DFID haka kuma mun ƙulla hulɗa da UNICEF wadda ta samu goyon baya daga DFID.

Bugu da ƙari mun ƙulla wata hulɗa da Jolly Phoeniɗ da wasu cibiyoyin bayar da horo waɗanda suka haɗa da JAKA wadda ke samun tallafi daga Hukumar Horas da Malamai ta Ƙasa wato NTI. Mun ƙulla hulɗa da JAKA ne domin bunƙasa yanayin koyarwa a makarantun mu.

Baya ga wannan Jihar Zamfara kaɗai ce a Nijeriya wadda ke ɗaukar nauyin malamai zuwa rangadin ilmantarwa. Kwanan nan mun ɗauki nauyin malamai 10 zuwa Ƙasar Burtaniya domin halartar wani shiri na ilmantarwa daga Jolly Phoeniɗ. Malaman waɗanda aka horas a yanzu haka suna nan suna horas da wasu malaman abubuwan da aka koyar da su a ƙasar ta Ingila. A taƙaice ma malaman mu ne ke bayar da horo ga wasu malamai a jihohin Kwara, Kaduna, Jigawa, Gombe, Taraba da sauransu a shirin ilmantarwa na Jolly Phoeniɗ.

Haka kuma idan ka yi duba ga wannan jihar za ka ga cewar ita kaɗai ce jihar da malamanta na firamare suke samun kuɗin hutu. Domin tun daga 2011 muna biyan su kuɗin hutu cikin lokaci.

Waɗannan ne hanyoyi da dama da muke ganin muna bayar da fifiko ga jin daɗin malaman firamare. Duk da yake dai har yanzu ba mu samar masu da abin da muke fata ba wato tabbatar da ƙarin mafi ƙanƙantar tsarin albashi. Abin da ya faru shi ne mun buga lissafi idan za mu ƙaddamar da ƙarin albashi mafi ƙanƙanta dole mu tabbatar mun liƙe duk wata kafa ta rashin biyan albashi. Idan muka ƙaddamar da tsarin kuma aka wayi gari ba mu iya biyan albashin ka ga akwai matsala don haka muka zaɓar masu abu mafi dacewa ba tare da riƙe masu kuɗi a ƙarshen wata ba. Amma kuma muna ƙoƙarin tabbatar da tsarin da zarar tattalin arziki ya inganta

Hukumar ka ta himmatu wajen canza fasali da sake gina makarantun firamare a faɗin jiha bakiɗaya. Abin jin dadi shi ne kwangilar naira bilyan 3.6 da aka baiwa ‘yan kwangilar gida a faɗin ƙananan hukumomi 14 da ke a wannan jihar. Ko za ka yi mana ƙarin bayani a kai tare da dalilin yin hakan?

Gaskiya ne Gwamnatin Jihar Zamfara ta hannun Hukumar Bayar da Ilimi Bai Ɗaya ta samu karɓar kuɗaɗe daga Hukumar Ilimi Bai Ɗaya ta Ƙasa na gudanar da ayyukan 2014/2015 a shekarar da ta gabata. Don haka muka fara shirye-shiryen bayar da kwangilar aikin agaji a makarantun mu na firamare da ƙaramar sakandire.

Kuɗaɗen kimanin naira bilyan 3.6 ne kamar yadda ka bayyana. A yanzu haka dai mun yi nazari domin gano yanayin da makarantun firamare da ƙaramar sakandire suke ciki waɗanda ke buƙatar gyara ko sabuntawa a faɗin jiha bakiɗaya.

Haka ma mun yi niyyar faɗaɗa waɗannan makarantun ta hanyar gina wasu ɗakunan karatu domin a rage cinkoson da makarantu ke fama waɗanda yara suka zarta adadi. Mun ɗauki dukkanin matakan da suka kamata domin ganin mun samu nasara a wannan shiri da muka ɗaura niyya.

Kimanin makarantu 114 ne za su ci moriyar wannan shirin na agaji. Haka ma za mu sayi kujeru da tebura guda 11, 887 ga yara. Haka kuma za mu samar da kujeru da tebur na zaman malamai domin ƙara samar da yanayin koyarwa mai kyau, su kansu za mu sayi guda 1, 456.

Wani muhimmin abu a wannan shiri shi ne a karo na farko a Nijeriya muna duban yadda za mu kyautata muhallin sashen mulki na Sakatarorin Ilimi domin ya zama ingantacce. Domin farawa aƙalla za mu gina ofisoshi guda 10 a Ƙananan Hukumomi 10 kuma za a inganta su da na’urorin fasahar sadarwar zamani wato ICT, haka ma za a sanya sabis na ‘Internet’ na awa 24 domin dai Sakatarorin Ilimi su samu damar gudanar da ayyukan su yadda ya kamata. Kimanin ‘yan kwangilar mu na gida 326 ne waɗanda ke zaune a  yankunan da waɗannan makarantun suke aka ɗauka domin gudanar da wannan aikin.

Leadership Hausa

Ko kun san tarihin Daular Zamfara? Karanta shi a nan - TARIHIN DAULAR ZAMFARA

Popular Posts