Thursday 12 October 2017

2. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

Daga HON. Ibrahim Muhammad Danmadami (Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsare-tsare na Jihar Zamfara)


Karanta na farko a nan > 1. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

Birnin Kanoma suma Katsinawa ne da  Sarakunan Tsohuwar Daular Zamfara suka Mulka. Bingi da Bini kuma Zamfarawa ne suka kirkire a Karkarshin Jagorancin Jekada Wanda shine Shugaban Gidan da Banaga Danbature Dan Dadau (Wanda Yayi Artabu da Fulani Torankawa Masu Jihadi ) a Karshen K'arni na 17 zuwa K'arni na18 Ya fito.

A Birnin Zamfara bayan Mutuwar Bakururu sai Bak'ara Ya gade Shi , Shi kuma  Gimshik'i ya gade shi. Daga Gimshik'i kuma sai Jikanyar Bak'ara , Argoje Wanda ta zamo Sauraniyar Zamfara(1350-1390). A lokacinta Zamfara ta Yak'i Azbinawa da Gobirawa ,ta kuma Samu Nasarori da dama akan su. Daga Argoje sai Karafau Dan Gimshik'i(1390-1410) Wanda  aka ce kusan Mulkinshi a Yak'e -Yak'e ya K'are ,musamman da Adarawa,har Mutanenshi sukan K'osa da yawan hare-haren da yake tura su suna kaiwa Makwabtanshi.

Gatama Dan Gimshiki ne ya gadi Karafau. Yayi Shekaru da dama akan Mulki.An kuma ce Hakimai da Al'ummar shi sun ji dadin Mulkin shi saboda baya son husuma. Sai Kudandan Dan Karafau Mai Yawan "Yaya da kuma al'adar tub'e Hakimai.Ance Zamfarawa Sun So suyi Mashi bore sai ya Mutu. Sai Sarkin Zamfara Bardau Dan Gatama, Sarki Mai Yawan Fara'a da son Jama'a baya son zalunci.Ance a lokacin shi Daular Zamfara ta K'asaita saboda Talakawa sun wadata sosai dalilin rashin zaluncinshi.

Gwabrau Dan Kudandan, Sarki Mai yawan Yak'i da Makwabtanshi , Musamman Azbinawa shine ya gadi Bardau. Ance wata rana Azbinawa suka kawo Mashi takakka har Birnin Zamfara, basu da labarin a shirye yake yana jiransu saboda yana da neman labarin Makwabtanshi. Ya fatattakesu. A lokacin shi Kasar Zamfara ta Samu Wadata saboda akwai yalwar abinci.Taskarinburum Dan Bardau ,Sarki Mai Son Zaman lafiya shine ya gade shi.  A zamaninshi Kasar Zamfara bata yi Yak'i ba, amma bai jima yana Sarauta ba ya rasu.

Durkurshi Dan Kudandan shine Sarki na 11 . Kasar Zamfara a lokacin shi bata Yak'i da Makwabtan ta ba,sai zaman lafiya.Mawashi Dan Bardau Ya gadi Durkushi, sai dai shi mai son Yak'i ne sosai. Ya addabi Zabarmawa da hare-hare ,amma dai bai cisu da Yak'i ba. Ya dade yana Sarauta Kafin ya mutu har ma Mutanen shi suka K'osa dashi saboda halinshi na Yak'e- Yak'e. Sai Sarki K'igaya Tabarau DanTaskarinburum, Sarki Mai halin Mahaifinshi na adalci. Baya son Yak'i, bai dade yana Sarauta ba ya rasu.

Daudufanau Dan Durkushi shine ke biye da K'igaya Tabarau. Ance adilin Sarki ne,Sai dai lokacin shi Sarauta ta rage K'arfi saboda ko in kula da yake nunawa har Makwabtan Zamfara suna kawo Mashi hari sosai. Mutanen shi sun K'osa dashi saboda wannan hali, amma bai jima yana Sarauta ba ,ya mutu.

Sarki Burunburun Dan Mawashi ya gadi Daudufanau a 1536. Mayakin gaske ne Wanda yakai Yak'i har bakin Kuwara. Ance a lokacin da ya isa Yawuri/Yauri ya tarad da Shugaban Jama'ar Wurin ya kashe Wani K'aton Kada,ya raba naman kada ga mutanen Tungar tashi. Ya Tambaya mi ne ne sunan Sarautar tunga suka gaya Mashi,yace daga wancan lokacin a cigaba da kiran Sarautar da Sarkin Yawara,ance shine dalilin da yasa Sarautar Yauri take Sarkin Yauri har ya zuwa yau.

...

Za mu ci gaba a nan > 3. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

Bukar Mada

No comments:

Post a Comment

Popular Posts