Thursday 12 October 2017

5. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

Daga HON. Ibrahim Muhammad Danmadami (Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsare-tsare na Jihar Zamfara)

  

Karanta na hudu a nan > 4. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

Sarkin Zamfara Yakubu Danfaskare (1734-1739) shine yazo bayan Sarki Babba. A zamaninsa ne Gobirawa suka dinga taruwa a Kasar Zamfara da sannu sannu. Sun sauka a gonar Alkalin Zamfara(Alkalawa)inda yake zaman noma, suka nemi iso wajen Alkalin Zamfara cewa suna so su zauna anan ,yace masu bashi ke da Kasa ba amma zaya nemar masu izni daga Sarki. Ya rubuta takarda zuwa ga Sarkin Zamfara yana mai sanarda shi cewa ga wasu  baki nan sun zo daga arewa wajen Kasar Azbin kuma suna neman yardar Sarki cewa su zauna anan tareda shi, domin ya ga zamansu anan zai yi amfani domin yaga manona ne kuma akwai Malamai a cikinsu. Sarkin Zamfara ya tara Majalisar sa ya gaya masu sakon Alkali,amma yace masu shi bai yarda su zauna a cikin Kasar sa ba domin kuwa Malaman sa sun dade da sanardashi cewa akwai wasu mutane da za su zo daga arewa su kwace masa mulki.

Ana cikin wannan hali ne sai Sarkin Zamfara Yakubu ya rasu,aka nada Sarki Gigama duk da yake bai dade yana Sarauta ba amma yak'i  amincewa da zaman Gobirawa a Alkalawa. Bayan sa sai aka nada Sarki Malu (1741-1758) wanda a lokacin sa yawan Gobirawa ya k'aru a yankin Zamfara domin kuwa sun samu amincewar sa cewa su zauna a gefen Birnin Zamfara. Samun haka , sai Gobirawa suka nemi ya aminta da su nada shugaba daga cikinsu domin yi masu shugabanci a inda suke zauna.Bai aminta da wannan bukata ba, bayan rasuwar Sarki Malu an samu dan tsaiko wajen nada sabon Sarki saboda Siyasar cikin Gida. Gobirawa sun yi amfani da wannan damar, suka yi shugabanci a inda suke zaune.

Da samun Wannan dama ce akace Gobirawa suka fara kai farmaki a wasu garuruwan Daular Kabi , daga karshe sai suka aukawa masu masaukin su,watau Zamfarawa har suka kwace Alkalawa da Birnin Zamfara. Wannan ya tilastawa Sarkin Zamfara Marok'i fita zuwa Kiyawa dake Kudancin Birnin Zamfara ya maida ita hedikwatarsa.A kiyawa , Sarki Marok'i ya kulla kawance da Katsinawa har ma suka bashi taimakon rundunonin Mayaka inda ya fuskanci Gobirawa a wani wuri da ake kira Dutsen Wake dake gabas da Birnin Kiyawa ,ya fatattaki Gobirawa sosai . Ya rasu akan gadon Sarauta sai aka nada Danbawa Dangado.

Sarkin Zamfara Danbawa ya soma tattara Zamfarawan da suka watse sanadiyar kwace Birnin Zamfara da Gobirawa suka yi,amma ance bai samu tara wani abin kirki ba. Ance ya kafa wani sabon wuri a Kuryar Madaro dake cikin Masarautar Kaura Namoda a halin yanzu.Amma Gobirawa sun hana shi sukuni sosai. Bayan rasuwarsa sai aka nada Abarshi Dan Marok'i(1805-1815). Shine Sarkin da ya tara Zamfarawa, amma kafin tarasu Gobirawa sun tab'a Kamashi tun yana Yaro K'arami su ka tafi dashi wajen Sarkin Gobir, watau tun kafi ya kai ga yin Sarauta.

A lokacin da Gobirawa suka lalata Birnin Zamfara, Sun kama Zamfarawa da yawa cikin su Kuwa har da Sarakai da Yayan Sarki. A cikin YaYan Sarki da suka kama har da Wani Yaro Dan Sarkin Zamfara Marok'i. Bayan sun kai shi wajen Sarkin Gobir, sun yi tsammani zai kashe shi ne, sai suka ji Sarkin Gobir yace "Wannan Yaro Abarshi, Allah ne Ya barshi, ma'ana abarshi da rayuwarshi ,kada a kashe shi. Daga nan ne wannan suna na Abarshi ya bishi . Ya Tashi a fadar Gobir, ya girma har ya soma aikawa Zamfarawan da suke warwatse a ko'ina suna dawowa Birnin Zamfara/Alkalawa, wasu kuma suna dawowa a K'ashin Kansu. Ya cigaba da tara dawaki da kayan Yak'i a b'oye. A lokacin da Gobirawa da Sarakunan su suka fahimci haka, sai suka Kore shi daga K'asar.

Wannan shine Sarkin Zamfara Abarshi Dan Marok'i.Bayan Gobirawa sun koro shi ,sai ya taso ma yammacin Zamfara har ya iso Tumfafi ta Kasar Talata Mafara. Ya nemi izni ga Sarkin Mafara cewa yana son ya zauna anan tareda Jama'arshi. Sarkin Mafara ya amince masa. Ance bayan sun zauna anan Tumfafi, Sarki Abarshi ya ziyarci Mijaddadi Shehu Usman Danfodio a Sifawa. Bayan dawowa daga wannan ziyarar ne, akace Sarkin Mafara ya aiko masa da Kyauta maiyawa da kuma rokon arziki cewa ya tashi ya bar mashi Kasarshi saboda dama shi Sarki Abarshi Ubangijinsa ne,saboda haka baya jin dadin zama kuda da Ubangijinsa.
Bayan Sarkin Zamfara Abarshi ya samu wannan Sak'o na Sarkin Mafara ance ya tara Jama'arsa ya sanarda su. Suka bashi shawarar cewa su tashi su bar masa K'asarsa. Sai Sarki Abarshi ya aikawa Sarkin B'urmin Bakura cewa yana neman wurin zama shi da Jama'arsa a K'asar Bakura. Ance ba tareda wani jinkiri ba ,Sarkin B'urmi ya tambaye shi a ina yake so ya zauna a cikin K'asar Bakura? Yana mai cewa dama ai K'asa ta Sarki Abarshi ce tunda shine ya yi masu(B'urmawa) izni suka zauna a inda suke zaune ,watau a Bakura(idan muka zo tarihin Daular Bakura, a cikin Daulolin da suka rayu a cikin tsohuwar Daular Zamfara, Insha Allah za a ji yadda B'urmawa suka Mallaki Bakura,wadda a wancan lokaci K'asa ce a tsohuwar Daular Zamfara).

Sarki Abarshi yace yana so su zauna a Sabongari(Sabon gari tana Kudu da Garin Bakura , kuma anan ne GSS Bakura take a halin yanzu). Sarkin B'urmin Bakura yayi murna sosai da ya ji cewa Sarki Abarshi ya nemi wannan buk'ata a wajen Sa. Ance da kansa ya fito tareda Jama'arsa suka shirya masu Masauki mai kyau a Sabongari. Bayan Kammala Shiri, Sarkin Zamfara Abarshi da Jama'arsa suka tashi daga Tumfafi zuwa Sabongarin Bakura. Ance bayan komawarsu da wata uku ne, Sarkin Zamfara Abarshi ya rasu.
...

Za mu ci gaba a nan > 6. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

Bukar Mada

No comments:

Post a Comment

Popular Posts