Thursday 12 October 2017

10. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

Daga HON. Ibrahim Muhammad Danmadami (Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsare-tsare na Jihar Zamfara)


Karanta na tara a nan > 9. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

K'asar Anka ta kusan kwashe Shekara daya bayan rasuwarsa bata da Sarki. Sai a watan Nuwamban 1994 ne aka nad'a wani Ma'aikacin Diplomasiyya na Najeriya,  Mai Martaba Alh Attahiru Muhammad Ahmad CON a matsayin Sarkin Zamfara Anka. (Dalilin da yasa aka kwashe kusan shekara daya babu Sarki a Anka (December 1993-November1994) , wannan kuma gwagwarmayar cikin gida CE. Watau Yayan Sarki sun duk'ufa wajen neman Sarautar ne , Allah bai kawo k'arshen ta ba sai November 1994)
Bayan an K'irk'iro Jahar Zamfara  ranar 1 ga watan Oktoban 1996, Gwamnatin Mulkin Soja ta Jahar, a K'ark'arshin Jagorancin Kanar Jibril Bala Yakubu Murabus ta kafa Kwamiti a K'ark'ashin Shugabancin Marigayi Malam Yahaya Gusau (Shattiman Sakkwato) domin ya fito mata da tsarin Masarautu da Kuma Sarakuna. Aka kuma sanya Marigayi Alh Muhammadu D'an Sanda Maru (Matawallen Maru) a matsayin Sakatare da kuma Alh Mohammed Bello Umar Karakkai mni (Matawallen Bungudu) Mataimakin Sakatare. Sauran mambobin kwamitin su ne: Marigayi Alh Shu'aibu Shinkafi,  Marigayi Alh Abubakar Tunau Mafara (K'ayayen Sardauna),  Alh BM Audu da kuma Alhaji Ibrahim Birnin Tsaba.

Wannan Kwamiti ya Kammala aikinsa ya kuma mik'a rahoto ga Gwamnati. Gwamnatin ta k'irk'iro Masarautu da yankunan Hakimai/Uwayen K'asa  a 1997, aka kuma nad'a  Sarkin Zamfara Anka , Mai Martaba Alh Attahiru Muhammad Ahmad CON a matsayin Sarkin Yanka mai daraja ta D'aya kuma shugaban Majalisar Masarautu ta Jahar Zamfara, Muk'amin da yake akai har ya zuwa yau. Saboda haka , duk cigaban da ya shigo Masarautar Anka tun Nuwamban 1994 zuwa yau , da hannunsa a ciki.

Ta fannin tattalin arziki kuma, kamar takwarorin ta da suka tasa tare , Tsohuwar Daular Zamfara tana tink'aho da noma da kiyo, saboda Allah Ya hore mata K'asar Noma mai tarin Albarka. Magabatan ta sun yi la'akari da yanayin K'asa mai albarkar noma da kiyon dabbobi irinsu Shanu da Awaki da Tumaki da Rak'uma da Dawaki . Musamman idan mukayi la'akari da tsoffin hedikwatocin su, zamu lura da suna kusa da Gulabe/Koguna. Misali, Dutsi da Birnin Zamfara /Alkalawa suna zagaye da Gulbin Bunsuru da Gulbin Gagare. Haka ma zamansu a Banga da Kiyawa da Kuryar Madaro da Sabon garin Bakura . Zuwan su Anka kuma sun samu mazauni kusa da Gulbin Zamfara da Gulbin Ka. Al'ummar ta kuma sun duk'ufa wajen fatauci irin na can da , watau trans sahara trade, saboda Sarakunan su sun kai farmaki na hare-hare har zuwa K'asar Ilori daga Kudu, Azbin da Adar daga Arewa ,Katsina daga Gabas , Kabi da Zabarma daga yamma da kuma K'asar Gwari da Nupe daga Kudu Maso Gabas.

K'ira da Jima da Fawa da Sak'a kuma sune K'ananan sana'o'in da suka taimakawa al'ummar wannan Daula wajen rik'e kansu a cikin Gida. Daga baya a zaman su na K'arshe a Anka, Allah Ya Wadata su da Ma'adinai Musamman Zinari a yankin Bagega. Duk da yake basu mori wani abin kirki ba a wancan lokaci ,farkon zuwan Turawa a 1903/1904 a yankin ya dad'a bayyana yawan irin Wadan nan Ma'adinai da ke jibge a yankin. Yanzu haka wata Hukuma dake K'asar Australia ta gabatar da wani bincike inda ta ke cewa Jahar Zamfara tana hasarar Zinari na Dala Miliyan 500 a kowace shekara ta hanyar masu gino sa ta haramtacciyar hanya. Galibin wannan Zinari yana fitowa ne daga wannan yanki na tsohuwar babbar hedikwatar tsohuwar daular Zamfara. Taken Jahar Zamfara a halin yanzu shine "Noma ne abin Tink'ahon Mu " Farming is our Pride.

...

An samu wad'annan bayanai ne a cikin wani Kundi da Wani Baturen Jamus, Mr. Kurt Krieger ya taskato a 1959. Sai 'yan k'are -K'are da aka samu ta hanyar hira da wasu muhimmman mutane da muka yi a lokuta daban daban tsakanin 1991 zuwa yau. Ya kira wannan aiki nasa da "Sokoto Province, Northern Nigeria"

Yayi amfani da literature mai dama . Kad'an daga ciki sune: 1821, Review of Travels in Africa, JL Burckhardt and G.Molien , 1823- Travels of a Tartar (From the Royal Gold Coast Gazette ), 1932-33 - Labaran Hausawa da Makwabtansu, 2Bde ,Lagos, 1954- Amina Sarauniyar Zazzau(Zaria) Abadie, M. , 1927-Lacolonie du Niger(Paris) Arnett, E.J
Sauran sune: 1957 Tarihin Fulani(Zaria) , Junaidu , M (Wazirin Sokoto), 1909-10, A Hausa Chronicle. Journal of the African Society, 1920- Gazetter of Sokoto Province (London), 1922- The rise of Sokoto Fulani(Kano) , Backwell, H.F,
A cikin literature din akwai: 1927 - The occupation of Hausa Land (1900-1904)Lagos, Baikie, W.B, 1909- Northern Nigeria: Historical Notes on Certain Emirates and Tribes (London), Clapperton , 1938- Sokoto Provincial Gazetteer, Hartman, J.M , 1930- The Muhammadan Emirates of Nigeria(Oxford), Hornemann, F, 1830- Records of Captain Clapperton's Last expedition to Africa, bd II, Leo Africanus da kuma 1922- Notes on Tribes , Provinces, Emirates and States of the Northern Provinces of Nigeria(Lagos) , Thompson J.
...

Bukar Mada

KARSHE

Ko kun san Tarihin Kasar Dansadau? Karanta shi a nan > TARIHIN KASAR DANSADAU

No comments:

Post a Comment

Popular Posts