Thursday, 12 October 2017

3. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

Daga HON. Ibrahim Muhammad Danmadami (Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsare-tsare na Jihar Zamfara)


Karanta na biyu a nan > 2. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

Sarki Fatifati Dan K'igaya shine Sarkin Zamfara na 16. Tagwaye ne ,shi da Dan Uwanshi. Ance Dan Uwan Ya rasu ne wajen artabun neman Sarautar.Shi ma Sarkin bai dade akan Karagar Mulki ba ya mutu. Sai Sarki Taritu Dan K'igaya (1550). Ance Yayi Yak'e -Yak'e da dama, Musamman da Zabarmawa,ya yi ta samun nasara akansu. An ce wani Dan Uwanshi ne ya kashe shi saboda gabar su ta cikin Gida. Zartai Danburunburun ne ya gade shi, Zarumin gaske ne ,ya yi fada da Kabawa har ya yi kusan wata ukku yana gaba da Sarkin Kabi, sai da Wazirin Daular Kabi ya sasantasu. Bayan Mutuwar shi sai aka Nada DaKa Dan Fatifati,duk da yake yan watanni ne yayi akan Sarauta ya mutu,ance Zamfarawa sun ji radadin Mulkinshi. Sai Tasau Dan Zartai ,Sarki Mai hakuri da adalci. Bai yi wasu Yak'e-Yak'e ba a Mulkinshi har ya mutu.

Zaud'ai Dan Daka(1625) shine Sarkin Zamfara na 19, Mayak'in gaske,shine ya fara kai wa Katsinawa hari daga cikin Sarakunan Zamfara duk kuwa da sanin cewa Katsinawa Suna taimakonshi idan ya samu barazana daga Kabawa da Zabarmawa. Jama'arsa sun yi aniyar tub'e shi saboda irin wannan hali ,da ya samu labarin hakan, sai ya shirya kashe wasu Sarakunan shi masu ra'ayin cewa a tub'e shi,amma kafin ya aiwatar da aniyarshi sai ya mutu. Akwai alkawalin zasu ba Danshi Sarauta idan ya mutu,sai suka fasa su ka baiwa Dan Uwanshi, Aliyu.

Sarkin Zamfara Aliyu Dan Daka, Sarki na 21 ,shine Sarki,  Musulmi na Farko a Daular Zamfara. Ance shine ya fara gina Masallatai a cikin Birnin Zamfara da Kauyukanta. Zarumin gaske ne mai yawan alheri. Duk inda yaci da Yak'i ance yakan gina Masallatai a wuraren . Ya Shahara sosai a zamanin Mulkinshi .

Bayan Sarki Aliyu Ya rasu sai aka nada Hamitu Dan Tasau ,sai dai babu wani cikakken bayani game da Kwazo ko rashin kwazonsa har ya rasu. Sai Sarki Abdu Na Bawanka Dan Aliyu (1660). Shine Sarkin da ya fara Yaki da Kanawa. Ance wani lokaci har farfajiyar Kanawa ya kai da Yaki. Yayi Sansani kusa da Kano ,suka yi Watanni suna gwabzawa tsakaninsu. Ance saura kiris ya rinjaye su ,sai wasu daga cikin Sarakunan sa suka ci karfinsa cewa su koma gida sai wani lokaci su dawo su ci Kano. Suka dawo Gida, yana cikin shirin Komawa Kano karo na biyu ne Allah Ya Yi masa rasuwa.
Bayan rasuwar Sarki Abdu Na Bawanka sai aka nada Dansa Suleiman(1674). Ya Kudurin  cika nufin Mahaifinsa na Yaki da Kanawa,ya yi shiri na musaman akan wannan ,kwaram sai ga shi daga Yamma Kabawa sun afka masa da Yaki, abin Yayi tsanani sosai domin ance Kabawa sun tara Dawaki kusa Dubu Shida domin sun samu gudunmuwa daga Adar,suna kuma a tsakiyar karfinsu. Ance ya karya karfin Kabawa sosai ,ya halaka Mutanen su kwarai a wannan gwabzawar . Bayan ya dawo gida ne daga Yakin Kabi Allah Ya Yi Masa rasuwa sai aka nada Muhammadu Na Makake Dan Abdu Na Bawanka. Mutum ne Zarumi ,mai kwarjini. Zamfarawa sun so shi sosai ya kuma Yaki Kabawa da Zabarmawa da nasarori da dama ,ya kuma dade yana sarauta kafin ya rasu a baiwa Abdu Dan Suleimanu wanda bai dade akan gadon mulki ba ya rasu. Ance dan lokacin da yayi yana sarauta ya fadada yawan Birnin Zamfara. Mutun ne Karimi,yakan yanka shanu Ashiri a kowace rana saboda rabawa musakai. Yana yi wa Sarakunan sa kyauta sosai, ba a samu Sarki mai kyautar garali ba a cikin Sarakunan Zamfara irinsa ba.

Usman Dan Muhammadu Na Makake shine ya gadi Abdu Dan Suleimanu . Sarki Mai adalci da son zaman lafiya. Zamfara bata yi wasu yake-yake ba a lokacin sa,sai dai Sarakunan Yakin sa basu so shi ba akan wannan amma Talakawa sun so shi kwarai dagaske saboda adalcinsa har ya zuwa rasuwar sa akan Karagar Mulki. Babba Dan Muhammadu Na Makake (1715) shine ya gadi Sarki Usman. Mayakin gaske, ya dami Zabarmawa da Kabawa da yaki. Yayi shirin Yaki dagaske ta hanyar Tara dawaki da takubba da masu da lifida da bindigogin da ya samo daga Bida. Kafin fita Yakin Kabi ance ya tara Malamansa suka yi masa rokon Allah domin yasamu nasara akan Kabawa. Ya samu gagarumar nasara domin baya ga dawaki fiye da Dari biyar da ya kwato da bayi maza da mata masu yawa har hakiman Kabi guda uku ya kamo. Bayan dawowa daga wannan Yaki,ya baiwa Malamansa Kyauta mai yawa ta bayi da dawaki da sauran abubuwa masu yawan  gaske . Ance Masartan sa suna yi masa kirari " Babba Dan Muhammadu, garwashi kafi kumurya" saboda tsananin Yakin sa. Yadade yana sarauta kafin Allah Ya Karbi abinsa.

...

Za mu ci gaba a nan > 4. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

Bukar Mada

No comments:

Post a Comment

Popular Posts