Thursday 12 October 2017

9. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

Daga HON. Ibrahim Muhammad Danmadami (Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsare-tsare na Jihar Zamfara)


Karanta na takwas a nan > 8. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

Abdu Caccabi D'an Muhammadu D'an Gigala (1904-1916) shine aka nad'a Sarki bayan rasuwar Sarkin Zamfara Gado. A zamaninsa ne akayi rabon K'asa zuwa Gundumomi (Districts). A cikin wannan aiki ne aka mayar da wasu garuruwan dake K'ark'ashin Anka zuwa wasu Gundumomi. Gwashi da Adabka da Matsafar Mudi(Masamar Mudi) aka mai dasu a gundumar Bukkuyum, aka baiwa gundumar Talata-Mafara garuruwan Gwaram da Jengebe da Babban Baki , Gundumar Bakura aka bata garin D'akko sai Gundumar Kuyambana da aka baiwa garuruwan Bind'im da D'angulbi.Bayan Shekara goma sha biyu yana sarauta sai wadansu Mutanen yankin Bagega suka yi K'arar shi a wajen  Sarkin Musulmi saboda zalunci. Aka yanke masa hukuncin tub'ewa daga Sarauta,a ka maida shi a garin Jangebe ta K'asar Talata-Mafara a inda Allah Ya Yi masa rasuwa.
Bayan cire Sarki Caccabi ,sai aka nada Muhammadu K'atar Mainasara D'an Hassan(1916-1928). A zamanin Mulkin sa ne Sarkin Musulmi ya sa aka sake duba iyakokin K'asar Anka da Sauran Mak'wabtanta ,aka dinga kafa alamomi a kan bishiyoyi da yin layuka na duwatsu saboda tantance iyakoki, domin mak'wabtansa sun kai k'ararsa a Sakkwato cewa yana ci masu iyakar K'asa. A zamaninsa ne a kayi godaben mota wanda ya tashi daga Gusau ya ratsa Anka har zuwa Jega,haka ma a Mulkin sa ne aka bud'a cinikin auduga da gyada a Anka kuma kamfuna irin su John Holt suka fara bude ciniki a K'asar Anka. Ya rasu yana akan sarauta bayan ya shekara Sha biyu .

Daga Sarki Muhammadu K'atar sai Sarki Muhammadu Fari D'an Abubakar Bawan Adam (1928-1946). Yayi Sarauta Shekara Goma Shatakwas da wata shida. A lokacinsa ne ciniki da Turawan G.B.O da U.A.C ya k'ara hab'aka har ma suka kafa wani Kantinsu mai suna London and Kano. Ance a zamaninsa ne Turawa masu ginar zinari suka shigo K'asar Anka ,haka wadanda suka kafa Gidan sayen fata a  lokacin Sa  ne suka shigo. K'asar Anka ta daukaka sosai a zamanin mulkinsa. An bud'e Makarantar Boko da ofishin Uban K'asa . A lokacin Sa ne akayi godaben mota daga Anka zuwa Dangulbi zuwa Dansadau. Ance saboda gargadinsa zuwa ga Talakawa akan su rike noma, Kasar Anka ta wadata da abinci a lokacin Mulkin sa, Fatauci kuma ya hab'aka. Ance a lokacin sa ne B'arawo baya sata a Anka, ance idan ma yayi sata daga wani gari ya shigo Anka ,to ana Kama shi. An cire shi Sarauta saboda tsufa.

Daga Sarki Muhammadu K'atar Sai aka Nada Ahmadu Barmo D'an Muhammad K'atar(1946-1965). Sarki Ahmadu Barmo shine Mahaifin Hafsatu ,wacce itace Mahaifiyar Gwamnan Farar Hula Na farko a Jahar Zamfara, Sanata Ahmad Sani(Yariman Bakura, Sardaunan Zamfara). A Zamanin Sarki Ahmadu Barmo ne aka sake duba iyakar K'asar Anka da Makwabtan ta. Aka sake rage ta a yankin Barayar Zaki a ka baiwa K'asar Bukkuyum. A zamaninsa aka Gina Asibiti da gidajen N.A a Anka. An kuma Gina riyojin Murtsatse ,aka kuma K'ara fad'in godaben Mota da kuma dasa itatuwa akan godaben. Ance sanadiyar wata hatsaniya, an jingine shi har na tsawon shekara biyu, kafin a gama binciken lamarin. A duk tsawon binciken, Sarki Ahmadu Barmo ya na Sakkwato ,yana neman ilmin Addini. Bayan Kammala binciken, an nemi ya koma akan Sarautar sa, ya k'i amincewa, yace yayi murabus. An ce an nemi ya koma akan Sarautar ne saboda ba a same shi da wani laifi ba, ko kuma laifin da ake tuhumarsa dashi ba(Duk da yake ba a bayar da takamaiman bayani ba akan laifin da aka tuhume shi da shiba,amma mazowa tarihin sun yi hasashen sha'anin Haraji ne ko kuma Jangali)
Bayan k'in Amincewar Sarki Ahmadu Barmo ya koma a kan Sarautar sa, a 1967 sai aka nada Alh Muhammadu Lawali Dan Ahmadu Barmo a Matsayin Sabon Sarkin Zamfara Anka, a lokacin shine Dagacin wani K'auye da ake kira Matseri. A Matserin ne ya haifi Sarkin Zamfara na yanzu, Alh Attahiru Muhammad Ahmad CON.

Sarki Muhammad Lawali ya sarauci Anka har zuwa watan Disamba na 1993 ,Lokacin da Allah Ya Yi Masa rasuwa. Tun daga 1967 zuwa 1993 , duk cigaban da Masarautar Zamfara Anka ta samu a fannona daban daban ,k'ok'arinsa ne.

...

Za mu ci gaba a nan > 10. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

Bukar Mada

5 comments:

  1. Zaifi kyaui dan aka sami wani wanda zai dora da kuma kawo cikakken tarihin Dukkanin Masarautun Kasar Daular Zamfara. A sahihance

    ReplyDelete
  2. Zaifi kyaui dan aka sami wani wanda zai dora da kuma kawo cikakken tarihin Dukkanin Masarautun Kasar Daular Zamfara. A sahihance

    ReplyDelete
  3. Mun gode sosai. Don Allah ina da tambaya, Hausawa ne ke sarautar Anka ko wasu kabilu?

    ReplyDelete

Popular Posts