Daga HON. Ibrahim Muhammad Danmadami (Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsare-tsare na Jihar Zamfara)
Tarihin Daular Zamfara ya faro da zaman Zamfarawa ne a Kauyen Dutsi da ke Masarautar Zurmi ta Jahar Zamfara, bayan sun yo hijira daga Kasar Gabas ta Tsakiya a Karni na 13. An ce Zamfarawan farko mutane ne masu Girman gaske, har ana kwatanta su da Samudawa.
An ce sun shekara bakwai a Dutsi ba su da tsayayyen shugaba. Sai daga baya suka nada Dakka a matsayin sarkinsu. Bayan Dakka, an yi sarakuna guda biyar, 4 maza ne; Jatau, Jimir Dakka, Kokai Kokai da Dudufani sai kuma guda daya mace, Argoje/'Yargoje. An ce duka wadannan Sarakuna 6 masu girman jiki ne sosai. Misali shi Dakka An ce yana cin hurtumin sa a lokacin kalaci daya.
Girman jikin wadannan magabatan Zamfarawa kamar yadda aka yi bayani na iya tabbatuwa idan akayi la'akari da kaburburan da ake ganin anan ne aka bizne su, su 6, a nan Dutsi, domin kuwa ya zuwa yau din nan wadannan jibga-jibgan kaburbura na nan a Dutsin.
Bayan zaman su a nan Dutsi, har suka yi sarakuna 6, sai su ka je arewa da Dutsi, har su ka kirkiri wani birni kusa da garin Isa da ke Jahar Sakkwato a halin yanzu, a lokacin sarkinsu na 7 da ake kira Bakurukuru. Suka ci gaba da gina birni wanda daga baya ya zamo ginannen Birnin Zamfara mai ganuwa. An ce lokacin bunkasar wannan birni yana da kofofi guda 50, sai dai a halin yanzu burbushin ganuwar kawai dake kusa da kofar gabas ta shiga Isa ake yi shaidawa.
Sarki Bakurukuru a Birnin Zamfara , ya auri Diyar Sarkin Gobir ,Fara ,ta haifar Mashi 'Yaya 2, BaK'ara Wanda Ya Gade shi bayan Mutuwarshi da Kuma K'anen Shi Gogarma ,Wanda ya Nada wata Sarautar Daular da ake kira "Sarkin Yarwari".
Wasu Birane a Daular Zamfara ta Wancan Lokaci irinsu Kiyawa da Kannu sun samu ne a dalilin sun Samu ne sanadiyar fita daga Dutsi da Sarkin Zamfara Bakurukuru, Gimshikin Gidan Dakka yayi a Kusan Karshen K'arni na 13 ,zuwa Birnin Zamfara . Kannu da Kiyawa a halin yanzu suna cikin Masarautar Birnin Magaji a Jahar Zamfara da Matsayin su na Gunduma. Ma'ana , Zamfarawa ne da suka fito tareda Bakurukuru daga Dutsi ,amma suka yi Kudu da Birnin Dutsi,yayinda Bakurukuru da wasu Jama'arshi suka je Arewa har sai da suka kirkiri Birnin Zamfara. Zamfarawan da suka girka Birnin Kannu sun Lak'abawa Kansu Matsayin Sarautar "Karaf" ,su kuma wadanda suka kirkiri Kiyawa suka Lak'abawa Kansu Sarautar Sarkin Kiyawa. Idan muka zo tarihin Daular Zamfara a lokacin Jihadin Mijaddadi Shehu Usman Danfodio za Mu samu K'arin bayani akan iriren wadan nan K'ananan Birane na Tsohuwar Daular Zamfarawa dama irinsu Masarautun Kwatarkwashi da Tsafe ,wadanda su kuma Katsinawa ne da suka shigo a yankin a Karkashin Jagororinsu, Gemun Dodo da Abu Kwatashi a cikin karni na 14.
...
Bukar Mada
Za mu ci gaba a nan > 2. TARIHIN DAULAR ZAMFARA
No comments:
Post a Comment