Daga Ibrahim Bello Gusau IBG
Hausawa dai na cewa "in bera da sata, daddawa ma da wari" amma akasarin masu rubuce rubuce akan matsalar WAEC/NECO a jahar zamfara sun kuskure ma wannan karin maganar ta hausawa, wanda hakan yassa duk rubuce rubucen su akan matsalolin kin biyan WAEC da NECO, sunka karkata a wuri daya.
A wani bincike dana gudanar a matsayin dai daga cikin manyan dalilan da sunka zama na gaba-gaba wurin kawo cikas akan kin biyan WAEC da NECO akan lokaci, wanda da yawa daga cikin masu rubuce rubuce sunka manta ko basu zurfafa bincike akai ba, shine wata almundahana da shugabannin makarantun gaba da sekandari (Principals) hadin guiwa da jami'an kula da jarabawowi (exams officers) na makarantun ke yi, na yin aringizo wurin baiwa ma'aikatar ilimi hakikanin adadin yawan dalibban da zasu rubuta jarabawa daga kowace makaranta kuma a kowace shekara.
Sanan nen abu ne a wurin kowa cewa dalibbai wa'yanda ba yan cikin makaranta ba, wato (external students), basu cikin wa'yanda dokar gwamnati da dokar ma'aikatar ilimi ta jaha sunka aminta da abiyawa kuddin jarabawa.
Adadin yawan irin wadan nan dalibban da ake kira external students,a wani lokaci, su kan kusa zarta adadin yawan dalibbai yan cikin makaranta (internal students) yawa, ta yadda hakan ke kawo ma gwamnati cikas wajen biyan kudaden WAEC da NECO akan kari. Zaka samu a makaranta daya akwai dalibbai yan cikin makaranta (internal students) dake shirin rubuta jarabawa wa'yanda adadin su ba zai wuce 250 zuwa 300 ba (a matsayin misali) amma idan anka hada da dalibban cuwa-cuwa sai kaga adadin ya kai 600 zuwa 700 (ya danganta da girma ko yawan makaranta) kuma a haka za a turama gwamnati da list din su domin biya masu kuddin jarabawa.
Wadan nan dalibbai (external students) su kan biya kuddi daga #5,000 zuwa #5,500, wani lokacin ma har #6,000 ko #7,000 ta hannun jami'an kula da shirya jarabawa (exams officers) kuma duk wadan nan kudaden da wadan nan dalibban (external students) ke biya suna zuwa ne cikin aljihun/aljihwan shugabannin wadan nan makarantu hadin guiwa da jami'an shirya jarabawa (exams officers) amma ba a aljihun gwamnati ba, wanda hakan ya taimaka matuka ainun wajen gurgunta kokarin gwamnati na biyan WAEC da NECO akan kari babu tsaiko.
A wani yunkuri da tayyi a shekarar data gabata, gabanin rubuta WAEC da NECO ta shekarar 2016, Ma'aikatar ilimi ta jahar zamfara ta kafa wani kwamiti da zai zagaya dukkan makarantun gaba da pramare dake jahar nan domin kididdige hakikanin adadin yawan dalibban da zasu rubuta jarabawa wa'yanda doka ta aminta da su a matsayin dai daga cikin matakan ragema gwamnati nauye-nauyen biyan kuddin jarabawar dalibbai, amma ga dukkan alamu aikin wannan kwamiti baiyi nasara ba, kasancewa akwai zarge-zarge dake tasowa cewa akwai wasu jami'an ma'aikatar ilimi da ake kashe-mu-raba da su na wadan nan kudade da shugabannin makarantun sekandari ke karba a hannun wadan nan dalibbai ta yadda hakan ya gurgunta aikin kwamitin ba tare da samun wani kyakykyawan sakamako ba.
Idan ya kamata ace gwamnati na biyan kuddin WAEC da NECO da basu wuce #400m ko #500m ba (a matsayin misali), sai kasamu gwamnati na kashe zunzurutun kuddi har #800m ko #1bn (a matsayin misali) a duk shekara inda gwamnati ke hasarar #400m zuwa #500m a kowace shekara (a matsayin misali), duk a sanadiyyar cuwa-cuwar shugabannin makarantun sekandari da abokanin tarayyar su.
Irin wannan halayyar tasu, ta taimaka matuka ainun wajen gurgunta cigaban ilimin matasan jahar zamfara har anka wayi gari al'umma duk sun tattara, sun jibgama gwamnati da mai girma gwamna duk wadan nan laifuffukan ba tare da la'akari da abun da munka ambata ba.
Wata makida da wadan nan shugabannin makarantun keyi itace ; a duk lokacin da kwamitin ma'aikatar ilimi zai ziyarci makarantun su domin kididdige yawan dalibbai, zasu kwaso dalibbai yan aji 4 (SS 1), da yan aji 5 (SS 2) su hadasu da dalibbai yan aji 6 (SS 3) domin rikita yan kwamitin, ba tare da sun gano komai ba balantana su san hakikanin adadin yawan wadan nan dalibban.
SHAWARA
Ina baiwa ma'aikatar ilimi da gwamnati jahar zamfara karkashin jagorancin *Hon. (Dr). Abdul'aziz Yari Abubakar (Shattiman Zamfara)* shawara akan kafa wani tsayayyen kwamiti na musamman wanda zai dinga zagayawa a wadan nan makarantu a kowace shekara domin kididdige hakikanin yawan dalibban daya kamata gwamnati ta dinga biyawa kuddin jarabawa ba tare da samun dogon jinkiri ba.
Da fatar Allah yasa wadan da abun ya shafa su duba domin samun cigaban ilimin matasan mu cikin sauri da kuma samun cigaban jahar mu ta zamfara , cigaba mai dorewa.
Written and Compiled by
Ibrahim Bello Gusau Ibg
Zamfara State APC Social Media Organisation (ZASMO).
Also read MY ADVICE TO THE COMMITTEE CONSTITUTED TO ADRESS THE ISSUE OF MASS FAILURE (SSSCE) IN ZAMFARA STATE
No comments:
Post a Comment