Thursday, 12 October 2017

6. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

Daga HON. Ibrahim Muhammad Danmadami (Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsare-tsare na Jihar Zamfara)


Karanta na biyar a nan > 5. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

Bayan rasuwar Sarki Abarshi a Sabongari, ance Sarkin da ke bi masa shine Fari D'an Marok'i. Ance babu wani Yak'i da yayi da wata K'asa ,ya cika mugun hali da rashin d'aukar Shawara har ta kai ga matakin da Madawakinsa ya jagoranci mutane suka kashe shi. Sai Suka nad'a D'anbak'o D'an Abarshi(1815-1824). Ance lokacin da za a nad'a shi, an nuna masa gawar wanda ya gada , an kuma gaya masa cewa irin mugun halin da ya nuna masu ne sanadiyar kashinsa. Ance da ya ga wannan yanayi , sai ya basu sharad'i cewa idan sun gaji dashi kada suka kashe shi,amma ya yarda su tsige shi daga Sarauta.

Masu Zaben Sarki da Sauran Zamfarawa suka amince da Sharad'in da D'anbak'o ya gindaya masu ,suka nad'i shi Sarkinsu anan Sabongarin Bakura. Bayan nad'in shi,ance Mijaddadi Shehu Usman Danfodio Tagammadahullah Birahamatihi ya ziryaci Sabongari, Ya kuma yi Kwanuka yana yi masu Wa'azi  har da Masallaci ya gina a garin.

Ance bayan Mijaddadi Shehu Usman Danfodio ya bar Sabongari, sai Sarkin Zamfara D'anbak'o ya aiki wani Baransa da Sammu ya kai a Birnin Anka,Wanda a wancan lokaci Zamfarawa ne a karkashin Jagorancin Banaga Danbature Dandadau ke shugabanta , ance kuma yayi hakan ne saboda yana son ya koma can Anka da zama ne.

Ance Wanda ya tafi da sammun da ya shiga garin Anka sai ya nufi k'ofar Gidan Sarkin(a inda Fadar Mai Martaba Sarkin Zamfara Anka , kuma Shugaban Majalisar Masarautu ta jahar Zamfara yake mulki a halin yanzu)da Kab'akin tuwon da aka yi sammun da shi. Ance da dare ne ya isa garin,sai ya ajiye Kab'akin tuwon a K'ofar gidan Sarkin ya tafi abinshi. Da safe Sarki ya fito sai ya ga wannan Kab'akin tuwon, ance sai ya koma a cikin gida ya umurci iyalinsa da su d'aure kayansu ,ya kuma aikawa Sarakunan sa cewa kowa ya d'aure kayansa zasu tashi daga Anka. Bayan sun kammala , ance sai ya jagorance su,suka fita garin Anka duk da iyalansu zuwa kudu, Wannan Sarki Shine Banaga Danbature Dandadau. Sun cimma wata tunga da ake kira Wamba, ance sun so su zauna anan, amma suka cinna wa tungar wuta su kayi gaba har sai da suka kai wani gari da ake kira Bagega(Bagega a halin yanzu Gundumar Hakimi/Uban K'asa ce a Masarautar Anka)daga nan suka je har bakin Gulbi Ka ,da niyar wucewa zuwa gaba,sai zama yayi zama suka mai da wurin gari ,suka kirashi da Sabon Birnin Banaga (a halin yanzu gundumar Hakimi/Uban Kasa ce a Masarautar Anka). Bayan fitar Banagawan Zamfarawa daga Anka, Sai Sarkin Zamfara da Jama'arsa suka kwashe Kayansu daga Sabongari, suka tasarwa Anka,ya shige gidan sarautar da suka tarar ginanne . Anka kuma ta Kasance hedikwatar Zamfarawa ta K'arshe . Bayan Shekara ukku da dawowar su Anka,sai aka cire shi daga Sarauta bisa ga Sharad'in da suka yi a can baya. Ance ya koma wani gari Bardi a cikin Masarautar Bakura ,a can ya rasu.An kuma ce Wanda aka aika da sammu zuwa Anka sunansa Garangamau.

Bayan tub'e Sarki D'anbako, sai Zamfarawa suka nad'a D'an Gado D'an Abarshi ya maye gurbinsa. Shi kuma bai dad'e yana sarauta ba ya rasu. Sai aka nad'a Audu Tukud'u D'an Fari ,shima watansa ukku yana sarauta ya rasu.Amma ance kafin rasuwar sa yayi Yak'i Mai tsanani da Sarkin Mafaran Garangi.

Ana ganin Wannan Sarki na Mafaran Garangi(Mafarar Garangi tana Yamma da garin Mayanci dake kan titin Gusau zuwa Sakkwato, idan an wuce Maru, sai dai kasar Mafara ce ) shine Ali Jan Masari, D'an Sarkin Mafara Wanda ya fita daga Mafara tun suna a Tumfafi saboda matsalar rashin samun Sarautar gidansu ta Mafara. Ance ya k'uduri k'irk'ira tashi Mafara tunda ya rasa wannan. Shine aka ce ya kirkiri Mafarar Garangi,ya kuma nad'a kansa a matsayin Sarkin Mafaran Garangi, kafin daga baya ya je ya kirkiri Bukkuyum da Birnin Zoma , zuriyarsa kuma suka zarce suka kirkiri Gummi.

Ance gaba tayi tsanani tsakanin su sosai har Sarkin Mafaran Garangi ya d'auro yak'i ya tasowa Anka da fiye da doki dubu ,amma Sarkin Zamfara Audu ya samu labari kafin isowar su. Ance ya raba rundunarsa kashi biyu , kashi d'aya suka tarbi Sarkin Mafaran Garangi da Jama'arsa ,kashi na biyu kuma ya tura su Mafarar Garangi . A Lokacin da Sarkin Mafaran Garangi ya iso wani gari Birnin Tudu kusa da Anka , ana batun a farawa Kabsawa sai ga rundunar da ta tafi garin Mafarar Garangi sun dawo da ganima maiyawa saboda sun ci garin. Dawowar su kuma sai rundunar Sarkin Zamfara ta k'ara K'arfi. Jin labarin cewa a ci garinsa, ya tilastawa Sarkin Mafaran Garangi juyawa zuwa gida . Ya Samu Jama'arsa wasu sun watse , Sauran da suka rage ya tattara su yayi Kudu(shine ake kyautata zaton wannan hijara tasu ce ta Samar da Garuruwan Bukkuyum da Zoma da Gummi ).Ance bayan wannan Yak'i ne Sarki Audu Tukud'u D'an Fari ya rasu.

...

Za mu ci gaba a nan > 7. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

Bukar Mada

No comments:

Post a Comment

Popular Posts