Thursday 12 October 2017

TARIHIN KASAR DANSADAU

Daga HON. Ibrahim Muhammad Danmadamin Birnin Magaji (Kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na  jihar Zamfara)


Garin sadau wanda shine hedikwatar Masarautar D'ansadau in da Sarkin Yanka Maidaraja ta biyu ke Sarauta a Jahar Zamfara ta samu ne  ta hanyar kirkiro garin da wani Mafarauci mai suna "Sadau" wanda ya  fito daga wani K'auyen da ake kira Karauchi (Karauchi  na cikin K'asar Kuya bana, wanda zamu yi bayanin samuwarta nab gaba a cikin wanna batu da muke akai In Shaa Allah) ya yi. A wannan wuri ne Sadau ke gasa naman abin farautarsa,  daga baya ya kwaso iyalin shi daga Karauchi zuwa wannan wuri da ya lak'abawa "D'ansadau" a k'arshe Karshen K'arni na 18 zuwa farko farkon K'arni na 19.

Wannan gari na D'ansadau ya yi ta hab'aka har zuwa Shekarar 1922,  a lokacin da Turawan Mulkin Mallaka suka ciro garin Marab'u daga Masarautar Gusau suka had'a da Garuruwan D'an Gulbi da Bind'in da Mutunji, suka Sanya D'ansadau a matsayin hedikwata. Saboda wannan had'akar ce Majalisar Sarkin Musulmi daga Sakkwato ta dinga turo Mutane daga Sakkwato suna Mulkin wannan gunduma da lak'abin Sarautar Sarkin Kudun D'ansadau.

Anyi Sarakuna guda uku daga Sakkwato tsakanin Shekarar 1922 zuwa farko farkon 1990s. Sarakunan kuwa sune: Sarkin Kudu Usman Dan Sama'ila (wanda daga baya aka canja mashi wajen aiki zuwa Masarautar Gusau,  a matsayin Sarkin Kudun Gusau) sai kuma Sarkin Kudu Abdullahi Mai Kiran Sallah da Kuma Sarkin Kudu Muhammadu Atu wanda daga gareshi ne Sarautar ta koma gidan 'Yan K'asa (sai dai kuma ba zuriyar Sadau ba) wato a lokacin da Marigayi Alh Shafi'u Salihu daga Zuriyar Ango ne wanda ya kirkiri gidan Sarautar Daraga (Masu Mulkin Garuruwan Dan Gulbi da Dan Kurmi a halin yanzu).

A lokacin Sa ne D'ansadau ta samu d'aukaka darajar Sarauta, daga Hakimi /Uban K'asa zuwa Sarki Yanka Maidaraja ta uku. Bayan rasuwar Sa kuma sai aka nad'a Sarki Husaini Umar, shi ma daga Zuriyar Ango a matsayin Sabon Sarkin Kudun D'ansadau kuma shine Sarki a halin yanzu, an kuma d'aukaka darajar Sa zuwa Sarkin Yanka Maidaraja ta biyu a Shekarar 2004. Amma kafin hedikwatar Masarautar ta dawo D'ansadau wannan K'asa ana Kiran ta "Kuyambana"  ne.

Kuyambana kuma wani Mutum ne da ya fito daga wani wuri da ake kira Kurshi ta Katsina a Shiyoyin K'arni na 14 mai suna Kagarki ya kirkire ta. An ce da suka iso wannan K'asa suna lokacin Damina ne,  sun tarad da anyi hud'a a gonaki,  shi ne suka labari suna cewa "Ai wannan Kunyen Bana ne" ma'ana wannan hud'a ta wannan Shekarar ce. An ce sun had'u da wasu Mutane su uku a wajen wadan nan gonaki, suka tambaye su a ina zasu ajiye Kayan su,  sai suka ce masu ku ajiye wajen "Kunyen Bana",  bayan sun sauka a wannan wuri ne sai jama'a suka cigaba da taruwa har gari ya samu da Sunan "Kuyambana".

Daga Kagarki wanda shi ne farkon Shugaba da lak'abin Kuyambana,  an yi Kuyambana har guda 19 kafin wannan wuri ya tarwatse sanadiyar wasu gandayen Daji guda biyu da aka samar a wannan yanki wadan da suka kusan canye wajen noman al'ummar yanki (Kuyambana Game reserves).

Da wannan ne sai Al'ummar Kuyambana suka duk'ufa wajen kirkiro Sababbin garuruwa irin su Sangeku da Kakumo da Karauchi da Ranko da Ukambu da sauran su. An ce a lokacin Kuyambana na 13,  Musa D'an Damu ne Turawan Mulkin Mallaka suka amince da Sarautar Kuyambana a matsayin Sarki Maidaraja ta biyu, saboda kuwa an ce wani Bature da ake yi ma lak'abi da "Mai Tumbi"  ne ya yi bikin mik'a mashi Sandar Mulki a gaban Sarkin Musulmi da Sarakunan Kwantagora da Zazzau da kuma Birnin Gwari.

Kuyambana ta ci gaba da kasancewa a hakan har zuwa Mulkin Sarki na 17, Wato Kuyambana Zakariya'u. Bayan tarwatsewar Kuyambana ne,  wasu zuriyoyin wadan da suka kirkiri Kamar su Malam Ango suka fantsama a cikin K'asar har Sa da suka samar da garuruwa irin su Dankurmi (wadda ita kuma K'asar ta ce ake yi ma lak'abi da "Daraga") da Dangulbi da sauran su.

Bayan Garin D'ansadau ya Kasance sabuwar hedikwatar K'asar kuma a Shekarar 1922,  sai Mulkin Kuyambana ya cigaba a wannan wuri,  musamman idan aka yi la'akari da nad'in da aka yi ma Sarkin Kudu Marigayi Alh Shafi'u Salihu a Cikin farko farkon 1990s daga Zuriyar Ango daga garin Dangulbi (Ma'ana bayan Wadan da aka turo daga Sakkwato su uku sun Mulkin K'asar a garin D'ansadau). 

Zamu ji yadda sauran garuruwan K'asar Kuyambana ta D'ansadau masu farawa da "D'an"  a cikin sunayen su suka samo wannan lak'abi na "D'an"  a nan gaba In Shaa Allah.

Bukar Mada

Ko kun san Tarihin Daular Zamfara? Karanta shi a nan > 1. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

9 comments:

  1.  The fact of Planet-X, the planet of chastisement from the decisive Book as a reminder to the possessors of understanding-minds..


    - 1 -

    Imam Nasser Mohammad Al-Yemeni 

    27 - 11 - 1430 AH
    15 - 11 - 2009 AD
    12:26 am

    ReplyDelete
  2. Wannan tarihi ne da yake da muhimmanci sosai ga alummar jahar Zamfara da kuma masu shaawar da Nazarin tarihi.

    ReplyDelete
  3. Allah yakara albarka ga kasar Dansadau da kasa baki 1

    ReplyDelete
  4. Alhamdulillahi, lalle mai rubutu yana kan hanya dangane da tarihin masarautar Dansadau, domin kamar yanda ya nuna tarwatsewar Kuyambana shi ya haifar da Dansadau, kuma lalle mahukuntar Daular Usmanu Danfodiyo, su ne suka debo wurare dabam- dabam daga yankunan Gusau da Anka dama Bungudu aka kafa Gundumar Dansadau. Shi kuma Yasa kamar yadda suka yi ( Masu rike da gidan Shehu Danfodiyo a Sakkwato) a wasu masarau na yankin Arewa Nijeriya, suka tura tsatsonsu domin su rike musu sabuwar Gundumar Dansadau. Sa'anan tun da aka kirkiro da Gundumar Dansadau, sau iku a jèrè mahukuntar Daular Usumaniya ne suke mulkinta, domin su suke da abinsu a tarihin é. Bugu da kari, a wajen kafuwa da mulkin Masarautar Dansadau, babu wasu masu hakki irin Sakkwatawa su da suka assasa ta. Kuma dukkan wannan al'amarin ya wanzu ne kafin samun 'yancin kan Nijeriya. Kowa ya sani, a masautu da dama na Arewa ayau koma ince mago yawansu, Sakkwatawa ne ke mulkinsu, saboda abin ya samo.asali tun daga kafuwar Daular Usumaniya. Saboda haka, babu maganar wasu 'yan kasa' a tsarin sarautar Dansadau. Insha Allahu nan gaba kadan za'a fitar da ingantaccen tarihin wannan masarauta tare da kari bayani, akan matsayin yankunan dake cikin Masarautar.

    ReplyDelete
    Replies
    1. Su wakilan da aka tura Dansadau zuriar shehu usumanu ne ko dogarawa ne? Toh su ina ne garinsu I da kakaninsu da uwayen su Ina be danginsu cikin kasar Dansadau

      Delete
  5. Masha Allah, wannan Tarihi ne daya kamata ace duk wani Dan Dansadau emirate ya dace yasan dashi, Allah ya kawo mana xaman lpy Mai dorewa a qasarmu da sauran qasashen musulmai baki daya alfarmar fiyayyen halitta ma'aiki S A W 🙇 💝 😊

    ReplyDelete
  6. Ai wannan tarihin yanada muhimanchin sosai Kuma babu Wani bako daya gadi sarautar Dansadau baya ga yan kasa wandanda sune majalisar sarkin musulmi Ibrahim Dasuki ta aminta dasu bayan mayarda sarautar ga yankasa masu godonta na asali sune kuyanbana Daraga da Kuma karauchi kamar yanda circular ta nuna duk wakilan da aka turo ba yankasa bane kamar yada aka tura su irin Gusau da mada da talatar Mafara. Dansamaila ma a chanza masa garin wakilchi daga Dansadau zuwa Gusau,haka Kuma Muhamadu Atu daga mada aka turashi dansadau a tarihi baayima sarki Transfer

    ReplyDelete
  7. Hakika wannan tarihi yakamata duk Wani dankasa yafahinceshi dakyau saboda yasan yancinsa akasarshi saboda kasar dansadau Kasace waddda mutanen kasar keda hakki akanta kawai Babu wani bako ko wakili Wanda zaizo yace waishi keda hakkin sarautar dansadau alhali baida Wani tarihin dazai nuna inda kakanninsan da uwayensa suke musamman awannan yankunan kamar haka(1)kasar karauchi (2) kasar kuyam bana(3) kasar daraga (4) kasar marabu
    Dazarar bakana cikin wanna zuriarba bakada wani hakki sarautar dansadau Emirates wakili baya sarautar ko ince dogari baya sarautar dansadau Emirates Kuma alhali bakada cikin ahlin Usman danfodion sokoto uwayenku dogarai ne da bayii wasu Kuma yaran sarkine daga karshe Ina kira ga duk wAni basakkwace da yayi hatatara da sa kanshi cikin ahlin dansadau Emirates nagode

    ReplyDelete

Popular Posts