Daga Abdulmalik Saidu Mai biredi
Yau Laraba 11-10-2017 ne, wata Kotu da ke zama a Jahar Kano za ta zata Cigaba da sauraren shari’ar da ake yi Tsakanin gwamnatin Zamfara da Matasa 1400 da ta dauka aiki, yau sama da shekaru uku ba ta biyansu, Albashi.
A cewar shugaban matasan LUKMAN MAJIDADI, ” Mun Kai Gwamnatin Jahar ZAMFARA koto ne, saboda zaluntarmu da ta yi ta hanyar tauye muna hakki da ta yi. Wanda a lokacin da ta dauke mu aikin wasunmu suna da madogara amma sunka baro ta bayan sun samu aiki a gwamnatin jahar. Amma Abun ban haushi yau sama da shekaru uku muna aiki, amma ba a taba biyanmu naira daya ba. Duk da cewa, mu ne ma’aikatn da anka fi dauka ta sahihiyar hanya a Jahar zamfara. Wanda sanadiyar haka mafiya yawanmu a tagayyare mu ke yanzu.
“Dan haka mun sha alwashin zage Damtse har sai mun tabbatar da kotu ta kwato muna hakkokinmu” a cewarsa.
Zamfara Forum
11/10/2017
No comments:
Post a Comment