Daga HON. Ibrahim Muhammad Danmadami (Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsare-tsare na Jihar Zamfara)
Karanta na shida a nan > 6. TARIHIN DAULAR ZAMFARA
Sarkin Zamfara Abdu Fari D'an Abarshi (1825-1829) ne ya maye gurbin Sarki Audu Tukud'u . A Shekaru Hud'u da yayi yana mulki babu wani Yak'i da yayi da kowane Sarki ko kuma wata K'asa ba. Sai Sarki Abubakar Bawan Adam D'anbak'o(1829-1853). Shine Sarkin da ya fad'ad'a garin Anka a gefen Kudu, ya kuma yak'i garuruwa da dama a lokacin mulkin sa,watau garuruwan da ake kira K'asar Zoma/Zauma irin su Kaiwa, Birnin Tudu , Birnin Magaji, Nasarawa, Birnin Fulani, Kali, Bukkuyum, Makokoci, Kagali, Leshi, Fanda, Falale, Kaidaji, Dargaje da Birnin Zoma/Zauma.
Ance ya ci garuruwan da ake kira K'asar Zugu irinsu Danko, Kado, Zarummai, D'angurunfa daFarnanawa. Ya Kuma ci K'asar Gummi bayan ya shekara biyu yana yak'ar ta,saboda ance Sarkin Mafaran Gummi yana da runduna mai baraden yak'i da Doki fiye da dubu. Ya kuma Zarce har K'asar Kebb'e ya cinye ta. Bayan Shekara d'aya da daworsa daga wadan ne Yak'e -Yak'e ne akace ya sake shiri sosai ya nufi kudu har sai da ya cinye K'asar Kuyambana, ya kama Sarkin su ya dawo dashi Anka ya nad'a shi Sarkin K'ofa saboda ance ya nuna masa taurin kai. Ya abkawa K'asar Gwari ya kuma cinye ta har sai da ya kai Kurigi. Bayan dawowar sa gida kuma sai ya sake fita zuwa gabashin Anka har sai da ya kai Faskari ta K'asar Katsina. Daga arewa kuma ance duk garuruwan Zamfara sai da suka dawo cikin ikonsa. Ance a duk cikin Sarakunan Zamfara da suka yi Mulki a Anka babu Wanda ya kai shi Mulkin Jama'a kamar shi domin kuwa ance duk inda ya tsayar da al'ummarsa basu da halin yi masa musu har ya zuwa rasuwar sa.
Bayan rasuwar Sarki Abubakar Bawan Adam sai aka nad'a Muhammadu D'angigala D'an D'an Bak'o(1853-1877). Ba a dad'e da nad'a sa ba sai K'asar Zugu ta yi masa tawaye. Ance ya shirya rundunar Yak'i ya nufe su, ya cinye su ya kuma rushe gidan Sarkin su, ya kama mutanen K'asar Masu yawan gaske, ance Sarkin ma da k'yar ya sha, ya tsere ya nufi Gummi inda Sarkin Mafaran Gummi ya nemar masa ceto a wajen Sarki D'angigala. Ance ya hak'ura ya k'yale shi,amma bai yarda ya dawo Zugu ba ,saboda haka sai ya zauna a Dangurunfa yaci gaba da sarautar sa. Bayan wani d'an lokaci kuma yana a D'angurunfa sai ya koma tayarwa Sarki D'angigala da k'ayar baya , Ya sake kai masa farmaki yaci D'angurunfa amma bai samu Sa'ar Kama Sarkin ba domin ya tsere ya nufi Sakkwato. Da wannan ne sai D'angigala ya nad'a Abarshi a Matsayin Sarkin Danko(Domin itace Sarautar K'asar Zugu a wancan lokaci) a nan D'angurunfa. Bayan Shekara Ashirin da hud'u yana Sarauta,sai Allah Yayi wa Sarki Muhammadu D'angigala D'an D'an Bak'o rasuwa.
Hassan D'an Muhammadu D'angigala (1877-1896) shine Sarkin Zamfara bayan Sarki Muhammadu D'angigala. Duk da yake bai yi wasu yak'e -yak'e ba a lokacin mulkinsa,amma ance a zamaninsa ne Sarkin Musulmi ya ba Anka "Gaba". Dalilin Gabar kuwa ance shine wata rana Mutanen Mafara suna fad'a da Mutanen Bakura akan wani gari Birnin Tudu(a halin yanzu Garin Gundumar Hakimi/Uban K'asa ne a Masarautar Bakura, yana akan hanyar Yar Bagaruwa/Yarkofoji/Danfanfo/Rini/Gorar Namaye/Magami/Janbako/Faru/K'aya/B'oko road)sai suka aika ga Sarki Hassan domin ya taimake su.
Ance Sarki Hassan ya aiko masu da gudunmuwar Masu Dawaki sosai. Su kuma Mutanen Bakura sai suka nemi gudunmuwa daga Sarkin Musulmi Abdurrahaman . Bayan su had'u an gwabza sai Mutanen Mafara suka samu galaba akan B'urmawan Bakura. Ance Mutanen Bakura sun gaya wa Sarkin Musulmi cewa a cikin rundunar Mafara fa akwai Mutanen Anka . Domin ya tabbatar da wannan Magana ance Sarkin Musulmi ya sa aka kamo wasu daga cikin rundunar Mafara ,sai kuma gashi an samu Mutanen Anka d'in a ciki.
Bayan Sarkin Musulmi Abdurrahaman ya tabbatar da wannan Magana ta Mutanen Bakura ,ance ya aikawa Sarkin Zamfara Hassan da takarda guda biyu,d'aya ta zaman lafiya ,d'aya kuma ta Yak'i yace ya zab'i duk wadda yake buk'ata.
...
Za mu ci gaba a nan > 8. TARIHIN DAULAR ZAMFARA
Bukar Mada
No comments:
Post a Comment