Thursday 12 October 2017

4. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

Daga HON. Ibrahim Muhammad Danmadami (Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsare-tsare na Jihar Zamfara)


Karanta na uku a nan > 3. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

Akwai bukatar a san cewa kafin  Sarkin Babba Dan Muhammadu yayi wafati , ya hab'aka daular Zamfara ta Shahara sosai har ta daina Kallon Uwar gijinta ,watau Daular Kabi da kima. Hasali ma sai da Zamfarawa suka turo Kasar Kabi ya zuwa iyaka da Birnin Kwanni ,arewa da Sakkwato ,nan kuma kudu har bayan Kasar Kebbe da Gummi har zuwa Gulbi Ka. Sarki Babba yayi K'awance da Muhammadu Dan Ciroma na Gobir da kuma Sarkin Azbin Gabba. Ya kuma saka Dansa Yakubu ya jagoranci wata runduna mai karfin gaske wacce ta karya lagon rundunar Kabawa har say biyu, har ma sai da ya kama Sarkin Kabi Ahmadu shi da wasu Kwamandojinsa ,ya kuma tsare su a kurkuku wannan shine kusan dalilin faduwar Surame, babban birnin Kabawa a farko Karni na 18. Bayan Yakubu Dan Babba ya zamo Sarki, Sarkin Kabi Hammadu ya kuduri cin Zamfara , an gwabza matsananci yaki tsakaninsu a Gandi da Tsamiyar Maibura . Sarki Yakubu ya samu nasarar Kashe Sarkin Kabi Hammadu a tsakanin Kogin Kuburi da Kyamu. A lokacin Sarki Yakuba Zamfara ta kawo karfi sosai ta rage wa Kabi karfi,ya cinye manyan garuruwansu kamar Gungu, Leka da Kuma Surame ,har ma ya  cinye kusan rabin Katsina.

A lokacin Sarki Yakubu Dan Babba ne wani abu ya faru har ya zama Karin Magana a Daular Zamfara. Ance wani Ba'azbine ya taso daga Azbin da Dokinsa zuwa Zamfara domin ya kawo ma Sarki Yakubu ya saya. Akan hanyarsa sai Dokin ya mutu, ya cire ragamar Dokin ya cigaba da tafiya har ya iso Birnin Zamfara. Ya yi gaisuwa ga Sarki, ya kuma gaya masa cewa ya zo da Doki ne ya kawo wa Sarki ya saya amma Dokin ya mutu a kan hanya. Sarki yace masa ya zo da ragamar Dokin? Ba'azbine yace eh, Sarki yace wa Sarkin Zagi ya karbi ragamar ya shiga da ita bargar dawakinsa ya gwada ragamar a Dawakin da ke ciki,duk Dokin da ragamar ta yiwa dai dai yazo ya gaya masa. Jim kadan Sarkin Zagi ya dawo ya gayawa Sarki cewa an samu Dokin da ta yiwa dai dai, Sarki ya tambaya nawa ne muka sayi Dokin, Sarkin Zagi yace shine Wanda muka saya Bawa Ashirin da Biyar. Sarki yace akai Bakon Masauki, bayan kwana biyu ya sa akirashi, ya sa aka bashi Bawa Ashirin da Biyar , kudin Dokin sa da Ya yi niyyar kawo masa,yace ai hasarar doki sai Sarki. Daga nan nefa Mutanen Zamfara suka rika cewa hasarar doki sai sarki idan anyi wani abu na Karin Magana. Ance yadade yana mulki kafin ya rasu.

Daga Sarki Yakubu Dan Babba sai Sarki Jirau Danbabba ya d'are karagar Mulki. Ance shi Sarki ne adili ,mai tausayi da sadaka da son zama lafiya. Bai yi wasu yake-yake ba a lokacin Milulkinsa duk da kuma ya dade akan Sarauta kafin ya rasu. Ance yakan tara Malamai yayi masu sadaka,yana kuma taimakon gajiyayyu da danginsa.Sarki Faskare Danbabba ne ke biye da Sarki Jirau a tsarin Sarakunan Zamfara. Mai son Yaki ne sosai domin ance a lokacin sa kusan kamar Sarakunan Yakinsa ke gudanar da Mulkin Kasar. Damuwa tayi yawa a tsakanin al'umma saboda yawan Yan Fashi da sauran miyagun mutane. Bai dade yana sarauta ba  domin wasu daga cikin danginsa suka yi masa makirci suka cire shi,amma kafin a bayyana masa cewa an cire shi sai aka iske ya mutu. Babba ne(1734)  ya maye gurbin Sarki Faskare. Ance Zamaninsa ne Gobirawa suka fara shigowa Kasar Zamfara,amma dai basu samu sukunin zama daram ba sai a lokacin mulkin Sarkin Zamfara Yakubu Dan Faskare (1734-1739) wanda ya gade shi.

...

Za mu ci gaba a nan > 5. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

Bukar Mada

No comments:

Post a Comment

Popular Posts