Daga Hussaini Baba, Gusau
Watakila ku so karanta wannan labari > ZA A CI GABA DA SHARI'A TSAKANIN GWAMNATIN ZAMFARA DA MATASA
Hukumar yaƙi da cututukan da ke addabar Ƙananan Yara da Mata da Alurar Rigakafin Cututuka watau (UNICEF ) ta ƙullla yarjejeniya da kafafen Yaɗa Labarai, ƙarƙashin Ƙungiyar ‘Yan Jaridu ta Ƙasa Reshen Jihar Zamfara watau ( NUJ) da Ma’aikatar yaɗa labarai ta Jihar a kan lalibo cutukan da ke addabar Ƙananan Yara da Mata a faɗin Jihar, don ɗaukar matakin kauda cutuka masu yaɗuwa a cikin al’umma.
Shugaban Hukumar UNICEF na Shiyyar, Sakkwato, Dakata Muhammad Muhiyidini ne ya jagorancin taron yarjejeniyar a ɗakin taron Malaman Firamare da ke Gusau.
Dakta Muhammad Muhiyidini ya bayyana cewa hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinga, don haka ne Hukumar UNICEF ta shiriya wannan taron yarjejeniyar ga kafafen yaɗa labarai don su shiga lungn da saƙo na samo rahotanin abubuwan da ya addabi al’umma don magance su.
“Muna kira ga ‘yan Jaridu da su taimaka wajen gano cutukan da suke addabar ƙananan Yara da Mata, da kuma wayar da kan al’umma wajan amsar allurar rigakafi, cutar shan’inna, ƙyanda da baƙon dauro don magance su. Kuma wannan Hukumar na nuna matuƙar farin ciki ta na samun wannan yarjejeniyar. Kuma anan take Hukumar da cigaba da wa Mahalarta taron bita na wuni uku.
Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jaridu na Jihar Zamfara (NUJ) Kwamared Mainasara Ɗansarki Ruwan Ɗorawa, ya bayyana cewa Wannan yarjejeniyar ta zo kan gaɓa na shirin Ƙungiyar wajen gano matsalolin al’ummar Jihar don magance su. Kuma ƙungiyar za ta mutunta yarjejeniyar don cigaban al’ummar Jihar ta Zamfara.
Shi ma a nasa Jawabin Kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Alhaji Umaru Jibo Bukuyum ya bayyana cewa’ Kafafen yaɗa labarai sune ƙinshiƙin cigaban alumna kuma tini su ke ta ƙoƙarin wayar da kan aluma wajan amsar Rigakafin Cututuka.da faɗakarwar Kafafen yaɗa labarai ne aluma ke amsar Rigakafin Cututuka. Dan haka zamu ƙara ƙyaimi wajan wayar da akan alumna, da kuma sunga baƙowar Cutta su gagauta zuwa asibiti dan ɗaukar mataki.
Leadership Hausa
14/10/2017
14/10/2017
You may also like to read this related story > EFFECTIVE HEALTHCARE AWARENESS: ZAMFARA TRADITIONAL LEADERS WANT WOMEN GROUP TO TAKE THE LEAD
No comments:
Post a Comment