Thursday, 12 October 2017

8. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

Daga HON. Ibrahim Muhammad Danmadami (Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsare-tsare na Jihar Zamfara)


Karanta na bakwai a nan > 7. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

A lokacin da takardun Sarkin Musulmi Abdurrahaman suka riski Sarkin Zamfara Hassan ,ance ya zab'i ta zaman lafiya saboda yace shi kam bai iya gaba da Sarkin Musulmi. Bayan Masu kawo sak'o sun fito fadar Sarkin Zamfara,sai Ajiyansa, Ibrahim ya biyo su ,yace su kawo takardun. Suka bashi ,ance sai ya yage ta zaman lafiya, yace su kaiwa Sarkin Musulmi ta Gaba, ya kuma aikata haka bada sanin Sarki Hassan ba.

Da komawar Manzannin Sarkin Musulmi da wannan Sak'o, Sai Sarkin Musulmi Abdurrahaman ya Sa aka yi shela Birnin Sakkwato da kauyuka cewa ya baiwa Anka Yak'i ,duk mai son Bawa ko Baiwa ya tafi Anka ya Kamo. Da jin wannan umurni na Sarkin Musulmi sai Sarakunan K'asar Zamfara suka shiga kwance alkawullan da Ke tsakanin su da Anka, ya kasance babu wani gari da ya rage a Karkashin mulkin Anka sai fa Matsafa (Wanda Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Na 18,Alh Ibrahim Dasuki ya canjawa suna zuwa Masamar Mudi dake cikin Masarautar Bukkuyum a halin yanzu).

Sarkin Zamfara Hassan ya fuskanci matsananci hali na yak'e -yak'e da hare-hare daga Makwabtansa, gabas da yamma ,kudu da arewa. Ance wannan hali ya kawo matsananciyar yunwa ,musamman ga mutanen Anka har ya kasance Yayan itace ne abincin su. Ance sai Manyan Garin suka yanke shawarar korar Sarkin Zamfara Hassan daga Anka domin su samu lafiya akan masifar da suka shiga akan yak'i da Sarkin Musulmi. Bayan sun yanke wannan shawara sai suka aikawa Sarkin Musulmi Abdurrahaman da wannan bayani nasu, shi kuwa Sarkin Zamfara Hassan da ya samu wannan labari sai ya fita garin Anka ya nufi wani gari da ake kira Gab'iya dake gabashin Anka(ana kyautata zaton wannan gari shine Gab'iya dake kusa Bini a Cikin Masarautar Maru a halin yanzu).

Bayan tafiyar Sarki Hassan, sai Zamfarawan Anka su ka nad'a Muhammadu Farin Gani D'an Abubakar Bawan Adam (1896-1899) a matsayin Sabon Sarkin su. Bayan nad'a sa, Sai Sarkin Musulmi Abdurrahaman ya bayar da sanarwar cewa babu sauran fitina tsakanin sa da Anka sai zaman lafiya. Ance ya aikowa da Sarki Farin Gani da Doki da Alkyaba a matsayi kyauta daga wajensa.Ya kuma bayyana cewa duk wanda ya tab'a kama mutumen Anka a matsayin bawa a lokacin da suke hatsaniya da Sarki Hassan ,to ya 'yanta shi domin yanzu gaba ta k'are tsakanin Sakkwato da Anka.

Sarki Farin Gani ya shiga gyaran zaman mutanen Anka. Jama'arsa suka samu natsuwa da zaman lafiya da walwala. Sarki Farin Gani ya sake gine Birnin Anka da ganuwa,domin kuwa ta rushe saboda yak'e -yak'e da hare-haren da suka sha fama da su a lokacin mulkin Sarki Hassan.Bayan sun samu lafiya, sai Sarki Farin Gani ya k'uduri cire Ajiya Ibrahim, Wanda shine ya assassa waccan gaba tsakanin Anka da Sakkwato. To dama ance Sarki Farin Gani ya kashe zalunci tsakanin al'umma ,musamman irin Wanda Sarakuna suke yi wa Talakawa . Sai Ajiya Ibrahim ya nemi goyon bayan wadan nan Sarakuna, ya k'ulla Makirci tare dasu ,suka cire Sarki Farin Gani, shi kuma ya koma wajen dangin Mahaifiyarshi a gidan Sarkin B'urmin Bakura ,inda ance ne ya rasu.

Bayan cire Sarki Farin Gani, sai aka nad'a Gado D'an Muhammadu D'angigala (1899-1904) a matsayin Sabon Sarkin Zamfara. A lokacin Mulkisa ne Turawa suka shigo Sakkwato. A lokacin Sa ne kuma babban godabe na mota mai fitowa daga Ikko ya biyo ta garin Anka, saboda kafin wannan lokaci babu mota ,babu jirgin K'asa sai Dawaki.Bayan ya shekara biyu akan karagar mulki ne ,turawa suka fara aikin titin mota da ya taso daga Zungeru ,hedikwatar Mulkinsu zuwa Anka,ance har ya iso K'asar Daraga a cikin Yankin Kuyambana, sai kuma aikin ya tsaya. Bayan Shekara biyar yana Sarauta, sai ya rasu.

...

Za mu ci gaba a nan > 9. TARIHIN DAULAR ZAMFARA

Bukar Mada

No comments:

Post a Comment

Popular Posts